Bichi da sauran gyaran Gwamna Ganduje —Enga Abubakar Bichi

28
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje

Hadimin gwamna Ganduje na Karamar Hukumar Bichi Eng Abubakar Kabir Bichi, ya godewa mutanen karamar hukumar bisa namijin kokarinsu wajen zaben Hon Sani Mukaddas barden Bichi, da matemakinsa Alh Shu’aibu Muhammed Fagwalo, a matsayin sabbin shugabanni tare da kamsiloli a zaben da aka gudanar a ranar Asabar din nan.

Eng, ya ce, wannan wata alama ce, Bichi tana tafiyar tsarin Gandujiyya, donhaka, ya yi kira ga mutanen karamar hukumar, su cigaba da marawa gwamna baya.

Cikin sakon bangajiya da ya rabawa manema labarai, Eng, ya nuna jin dadinsa, yadda aka gudanar da zabe cikin zaman lafiya.

” Mutanen Bichi mun yi godiya, kan zabo mutane na gari, kun yi mana komai, yanzu abin da ya yi saura ku yi mana gyara da zaben baba Ganduje, a zabe na gaba, domin cigaba da kawo ayyukan raya kasa”

 

 

Leave a Reply