Babban Asibitin Dawakin Tofa ya koma Asibitin sha ka tafi

58
ASIBITIN DAWAKIN TOFA
ASIBITIN DAWAKIN TOFA
ASIBITIN DAWAKIN TOFA
ASIBITIN DAWAKIN TOFA

Alummar yankin karamar hukumar Dawakin Tofa, daga Arewacin Najeriya, sun yi Allah wadai kan yadda babban Asibitin karamar hukumar  Dawakin Tofa Genaral Hospital, ya koma sha ka tafi.

Wani wanda ya bukaci a sakaye sunansa, ya ce  kimanin watanni uku da kammala kwangilar sabunta Asibitin, wanda gwamna jahar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar, amma har yanzu an kasa bude shi. ” Hakika abin takaici ne, yau kusan kimanin watanni hudu da kammala kwangilar Asibitin, amma har yanzu an ki budewa, kusan sau goma ana saka ranar budewa amma shiru abin ya gagara. Asibitin da aka samar domin kwantarwa ya zama sha ka tafi, hakika, marasa lafiya na fama, musamman mata masu ciki”

Wata mace mace mai suna Hajara, ta shaidawa HagoRadio cewa “Hakika mu na fama, musamman mata masu ciki, wani lokacin haka za mu zo Asibitin, amma babu gadon kwanciya, sai dai a tura mu Bichi ko Tofa”

Mun yi kokarin jin ta bakin dan kwangilar Asibitin, amma har lokacin hada wannan labari, ba mu same shi ba. Amma mun aike masa da sako ta waya, nan gaba za mu kawo mu ku ta bakinsa.

Leave a Reply