Ba don Ganduje ba da tuni jahar Kano ta rushe -in ji Alh Auwalu Yusif

18
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje

ALH_AUWALU_YUSIFWani dan kasuwar abinci ta Afrika da ke Dawanau Alh Auwalu Yusif, Dawakin Tofa, mai  fafutikar ganin cigaban  gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya sake nanata kudirin cewa, ya zama wajibi duk mai kishin kasa, ya jinjinawa gwamnatin Ganduje, kan yadda ya hana jahar Kano, rushewa duk da matsalar kudi da Najeriya ke fama.

Alh Auwalu, ya kara da cewa, jahohi da yawa ba sa iya biyan albashi bare samar da aikin raya kasa, amma ya ce gwamna Ganduje, dare da rana ayyukan da ya ke samarwa sun fi karfin lissafi, sabodahaka, ya yi kira ga Kanawa su sake zabarsa a karo na biyu.

A karshe, ya sake godewa wasu shugabanni da su ka hada da dan majalisar jaha Hon. Sale Marke, da dan majlisar tarayya Hon Tijjani Abdulkadir Jobe, da shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa, Hon. Ado Tambai, da Yusif Bashiri da kuma Ahmad Abas.

Leave a Reply