Auren dole ya jefa wata budurwa karuwanci

69
DAN KWALIN TURE KAGA TSIYA
DAN KWALIN TURE KAGA TSIYA
DAN KWALIN TURE KAGA TSIYA
DAN KWALIN TURE KAGA TSIYA

Lokuta da dama, batun auren dole kan samu lokaci mai tsawo al’umma na maganarsa, musamman matsalolin da ya ke haifarwa, amma abin mamaki haka zancen ke karewa a teburin mai shayi, ko kuma irin abin nan zancen banza bara na yi wake bana na yi harawa, domin har yanzu an rasa lalibo bakin zaran gyara, kuma kowacce rana wannan bakar dabi’a na cigaba da karuwa kamar wutar daji, amma abin tambaya wanene ya ke da laifi?

Babushakka, wannan tambaya ce mai tsauri kuma mai wuyar amsawa, domin dalilan da kan janyo yi wa mata auren dole su na da yawa, amma bari mu kalli kadan daga ciki, domin a lokuta da dama, wasu na danganta kwadayin kudi a matsayin wani jigo na yin auren dole, wasu kuma na ganin cewa watakila yabawa da tarbiyar mutum ya kan sa a dauki yarinya a ba shi ko ba ta so. Amma zance mafi karbuwa ya fi shahara da zafin bukata da kwalama irin ta wasu iyaye, marasa hakurin hadiye kwalama da a karshe garin neman gira a rasa idanu baki daya.

A rubutu na gaba, za mu kawo mu ku, matsalolin da auren dole ya ke haifarwa, musamman a wata ganawa da mu ka kai da wata budurwa mai suna Binta Kokakola, ‘yar asalin Adamawa mazauniyar Kano, wadda sanadiyar auren dole ta shiga karuwanci.

Leave a Reply