Asibitin Yakubu Dan NoNO Ya Samu Lambar Yabo

88
Dr. Nafi'u Yakubu
Dr. Nafi'u Yakubu
Dr. Nafi'u Yakubu
Dr. Nafi’u Yakubu

An yabawa wani Asibiti mai zaman kansa wato, Yakubu Dan NoNo Memorial Haospital, da ke garin Hedikwatar Karamar hukumar Tofa a Jahar Kano, yabon dai ya biyo bayan saukakawa marasa lafiya da kuma ririta su a kowanne lokaci, karkashin kulawar mai Asibitin wanda kuma shi ne babban likita Dr. Nafi’u Yakubu Dan Nono.

Shugaban kungiyar masu sana’ar kayan gwari ta jahar Kano reshen karamar hukumar Bichi, Malam Ali, shi ne ya yi yabon, a wata zantawa da wakilin Hago Radio Kabiru Inuwa, wanda a cewar sa ya zama wajibi a nunawa Duniya kwazon Asibitin, domin sauran likitoci su yi ko yi ” Babu abin da za mu ce da wannan Asibiti na Yakubu Dan NoNo Memorial Hospital, sai godiya da kuma shugaban Asibitin, domin aikin da za a yi maka a cikin birni a kan kudi dubu dari, a nan sai ya karbi dubu sha biyar a yi maka, sabodahaka mun gode Allah ya ja girma”

Wannan dai, kusan shi ne lokaci na farko da Hago Radio ta ji wani mutum na yabawa Asibiti da likitoci.

Leave a Reply