An yi artabu tsakanin Sanatoci da shugaban ‘yansanda Ibrahim Idiris

52
Shugaban 'Yansanda Ibrahim Idiris
Shugaban 'Yansanda Ibrahim Idiris

 

Shugaban 'Yansanda Ibrahim Idiris
Shugaban ‘Yansanda Ibrahim Idiris

A jiya Laraba shugaban hukumar ‘yansandan Najeriya Ibrahim Idiris, ya gurfana gaban wani kwamitin Majalisar dattawan kasar, domin amsa  tuhumar zargin da Sanata Isah Hamma Misau, ya yi masa.

Sanata Francis Alimikhena, daga jahar Edo, shi ne shugaban kwamitin binciken shugaban ‘yansandan, bayan gabatar da sauran mambobin kwamitin, sai ya bukaci   Ibrahim Idiris,   ya    kare kansa daga zargin da ake yi masa.

Rahotannin da su ka iske HagoRadio sun ce, nan take lauyan shugaban ‘yansandan Alex A Izinyon SAN, ya mike tsaye tare da cewa, “Ai babu wani bayani da shugaban ‘yansandan zai yi, domin tuni ya aikawa majalisar cikakken bayani a rubuce”

Jim kadan da sauraran jawabin lauyan, shugaban kwamitin ya soki kudirin lauyan, inda ya ce bashi da damar magana domin majalisa ba kotu ba ce, ba kuma shi ne shugaban hukumar ‘yansandan da ake tuhuma ba.

Yanzu haka dai, tuni majalisar ta dage zaman kwamitin zuwa wani lokaci, wanda daya daga cikin mambobin kwamitin Sanata Hope  Uzodinma, ya ce nan gaba za su sake kiran shugaban hukumar ‘yansandan.

 

 

 

 

Leave a Reply