An tsige mataimakin shugaban kasa

65
Tsohon mataimakin shugaban kasa Emmerson Mnangagwa
Tsohon mataimakin shugaban kasa Emmerson Mnangagwa
Tsohon mataimakin shugaban kasa Emmerson Mnangagwa
Tsohon mataimakin shugaban kasa Emmerson Mnangagwa

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, ya tsige mataimakinsa  Emmerson Mnangagwa daga kujerar mulki. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin ministan yada labaran kasar Simon Moyo, inda ya ce shugaban kasa Mugabe, ya dauki matakin tsige Mnangagwa, saboda keta dokokin kasa da kokarin tada zaune tsaye.

Rahotannin da su ka iske HagoRadio sun ce, mataimakin shugaban kasar ya dade yana fuskantar matsin lamba daga magoya bayan shugaban kasa Mugabe, da kuma uwar gidansa Grace.

Emmerson mai shekaru 73, kafin  zama mataimakin shugaban kasar Zimbabwe,ya kasance tsohon jami’in tsaro

Leave a Reply