An samu tsoho dan shekaru 110 yana hawa keke

53
IBRAHIM TELA
IBRAHIM TELA
IBRAHIM TELA
IBRAHIM TELA

Wani dattijo mai suna Ibrahim Tela, mazaunin karamar hukumar Dawakin Tofa a jahar Kano, dan kimanin shekaru dari da goma 110 ya zama abin mamaki, kasancewar duk  tsayin shekarunsa amma har yanzu yana sana’arsa ta dinki da kuma hawa keke wajen gudanar da zirga-zirgarsa.

A wata ganawa da wakilin HagoRadio Ibrahim Tela, ya ce abinda ya sa har yanzu yake da kuzarin hawa keke saboda Magin zamani be kashe masa jiki ba.  Yaro idan kana mamaki ka daina shekaru na sun kai dari da goma, kuma har wankin kaya ina yi, ina kuma zuwa gona, ina sana’ar dinki, ina kuma hawa keke idan zanje unguwa, ina so in gaya maka cewa ina da kuzari  domin Magin zamani da ku ke rambadawa abinci be kashe min jiki ba”

Ibrahim  ya gayawa HagoRadio cewa, har yanzu limamin masallacinsu ba ya riga shi zuwa sallar Asuba.

Leave a Reply