An nada ministan Whatsapp da Facebook

64
Shugaban kasa Mugabe
Shugaban kasa Mugabe

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, ya nada tsohon ministan kudin kasar Patrick Chinamasa, a matsayin sabon minista mai kula da harkokin Whatsapp da facebook.

 Shugaban kasar ya bayyan cewa, nadin ya biyo bayan matsin lambar da gwamnatinsa take fuskanta daga masu amfani da kafofin yada labaran zamani na whatsapp da facebook, inda ya kara da cewa nadin zai taimaka wajen dakile batagarin.

Sai dai tun bayan billar nadin ministan, al’ummar kasar Zimbabwe su ka shiga mamaki tare da yiwa nadin dariya.

Wannan dai shi ne lokaci na farko da wani shugaban kasa ya yi irin wannan nadi.

Leave a Reply