An lakadawa wata mayya dukan tsiya

60
hagoradiointernational
hagoradio

Wata bakuwa da aka danganta da mayya, ta sha dukan kawo wuka bayan da ta kama wata yarinya, a garin Hayinhago da ke yankin karamar hukumar Dawakin Tofa a jahar Kano.

Wakilin HagoRadio ya ce, matar wadda ake zargi ta shiga gidan wani mutum da ake kira Koli, da misalin karfe biyu na ranar Talata, bayan shigar ta gidan ta bukaci a taimaka mata da ruwan sha, amma kafin matar gidan ta debo  tuni ta damke kurwar wata yarinyar a gidan mai suna Hajjo.

Wakilin mu ya gana da mahaifiyar yarinyar inda ta  bayyana cewa ” Ni dai wannan mace ban san ta ba, ta zo ta ce a taimaka mata da ruwan sha, ina dawowa na iske yarinya ta Hajjo, tana suma, tana mama ta kama ni, ganin hakan na kwarma ihu, mutane su ka taru a kai ta dukan ta, a karshe ta ce, a saurara za ta dawo da kurwar”

Kan hakan wakilin mu, ya tuntubi wani malamin addini, don jin hukuncin maita a addinin musulunci. ” babu maita a addinin musulinci, amma akwai kambun baka, shi ya sa ake son duk lokacin da ka ga wani abu ya birge ka to ka ce tubarkalla.

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply