An kafa sabuwar APC a jahar Katsina domin tsige shugaba Buhari

52
Gwamna Aminu Bello Masari
Gwamna Aminu Bello Masari

Gwamnan jahar Katsina Aminu Bello Masari, ya ce an kafa sabuwar jam’iyar APC  mai lakabin APC AKIDA a jahar Katsina, domin yi wa jam’iyar PDP yakin nemen zabe da kuma kifar da gwamnatin Buhari.

Gwamna Masari, ya fadi haka ne a wata ganawa da manema labarai a birnin Katsina, domin mayar da martani ga jagororin sabuwar jam’iyar. Masari,  ya ce tuni  sun yi nisa wajen yaki da gwamantin Buhari, a wasu jahohi da  ya samu karbuwa ” APC akida a fakaice ba da ni su ke yaki ba, su na yaki da shugaban kasa Buhari,  domin har sun shiga wasu jahohi da ya samu karbuwa, su na yada mummunar manufarsu. kuma ni a matakin jahar Katsina abin da nasani in tabbatar an yi wa mutane aiki da kudadensu a fagen ilimi da lafiya da sauran hanyoyin rayuwa ba a diba a yi wasoso ba”

Leave a Reply