An hallaka shanu masu yawa a jahar Katsina

31
Makiyaya a wajen kiwo
Makiyaya a wajen kiwo
Makiyaya a wajen kiwo
Makiyaya a wajen kiwo

Wata sabuwar annoba ta barke a jahar Katsina,  lamarin da a halin yanzu ta hallaka shanun makiyaya guda takwas.  Wannan aL’amari ya faru ne a garin Hayin Sheka da Sabuwar kasa a yankin karamar hukumar Kafur, da kuma karamar hukumar Musawa.

Daraktan kula da lafiyar dabbobi na ma’aikatar gona da albarkatun kasa na jahar Katsina, Dr Isa Abba, shi ne ya fadi haka yayin wata ganawa da manema labarai, in da ya ce tuni sun yi wa dabbobin yankin rigakafi da ba su magunguna da  allurai don dakile yaduwar cutar a fadin jahar baki daya.

” mun samu wannan labari ne daga karamar hukumar Kafur, wanda an ce wani makiyayi dan asalin karamar hukumar shi kawo cutar bayan dawowa daga wajen kiwo a jahar Kwara, sai kuma karamar hukumar Musawa wanda shi ma wani makiyayi ya zo da ita daga jahar Bauchi”

A karshe Dr Abba, ya roki makiyayan jahar Katsina, duk lokacin da za su fita kiwo wasu jahohi su ringa sanar da ma’aikatar domin ba su wata kariya ta musamman.

Leave a Reply