An fara yanka mutanen Zamfara a matsayin shanu

31
SHANU A WAJEN KIWO
SHANU A WAJEN KIWO
SHANU A WAJEN KIWO
SHANU A WAJEN KIWO

Jahar Zaamfara na daya  cikin jahohin Najeriya, da aka yi amfani da addini wajen yaudarar mutane, domin samun nasarar siyasa, tare da alkawarin kawo canji.

Sai da ya zuwa yanzu Zamfarawa, sun fara   tofin Allah tsine ga mai uwa da wabi, kan yadda shugabannin da su ka zaba da nufin kawo sauyi, amma  aka wayi gari da lankwame rayuwarsu kusan kowacce rana  tamkar wasu shanu a ranar Salla.

Bukar Musa daga jahar Zamfara, a wata ganawa da wakilin Hago Radio, ya nuna takaicinsa kan yadda ‘yayan jam’iyar APC su ka yaudare su.

” Hakika APC a jahar Zamfara ta yaudare mu, domin an kai matsayin da mutane baki ba sa shigowa, saboda yadda ake hallaka mutane kamar shanu ranar salla”

Bukar, ya kara da cewa, yanzu dai  Zamfarawa, sun dauki aniyar kifar da gwamnatin APC a jahar Zamfara.

“Tuni  Zamfarawa, mun daina yadda ana cutar mu da dogon gemun karya, ana wasa da addini domin yaudara, donhaka 2019 Dr, Bello Muhammed Matawallen Muradun, za mu zaba, cikin jam’iyar PDP domin ya zo ya fitar da mutanen Zamfara cikin wannan mugun hali”

Leave a Reply