An bindige kakin PDP na jahar Adamawa

20
JAM'IYAR PDP
JAM'IYAR PDP
JAM'IYAR PDP
JAM’IYAR PDP

‘Yan bindiga dadi sun bindige kakakin jam’iyar PDP na jahar Adamawa Sam Zadock, lamarin ya faru ne lokacin da ya ke tsaka da tafiya  a cikin  mota tare da wasu mutane hudu, dai -dai lokacin da su ka isa  wani waje wanda da ya shahara da fadan manoma da makiyaya, a yankin karamar hukumar Demsa na jahar Adamawa.

Sakataren jam’iyar PDP na jahar Abdullahi Prambe, ya gayawa majiyar Hago Radio cewa,  kafin faruwar lamarin sun yi waya da shi.

“Kafin faruwar lamarin  lokacin da ya ke tsaka da tafiya, ya kira ni amma  daga karshe sai na samu labarin cewa an bindige shi”

Kakakin rundunar Sojoji Brig Gen, Texaz Chukwu, ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya tabbatar da cewa sun samu nasarar masu hannu cikin lamarin.

Leave a Reply