Akwai alamun Buhari zai sauka daga ministan mai

27
Shugaban kasa Buhari
Shugaban kasa Buhari

Jam’iyar PDP ta nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sauka daga mukamin ministan fetur, saboda matsalar karancinsa mai da al’ummar Najeriya ke fama tsawon watanni biyu.

Sakataren watsa labaran jam’iyar Kola Ologbondiyon, shi ne ya yi rokon a birnin tarayya Abuja, wanda a cewarsa shugaban kasar ya gaza ta fuskoki da dama.

“Yakamata shugaba Buhari, ya aje mukamin ministan mai, domin ya gaza ba zai iya ba, ya jefa ‘yan kasa cikin mtasala, haka ma bangaren tattalin arziki ya yi faduwar bakar tasa”

A iya cewa, idan shugaban ya ji rokon ,wata kila  ya kusa sauka daga ministan.

Leave a Reply